Yayin da cutar korona ta yi kamari sosai a harkokin sufuri na kasa da kasa, jiragen kasa dakon kaya tsakanin Sin da Turai na taka muhimmiyar rawa wajen zirga-zirgar jiragen kasa a tsakanin kasashe, kamar yadda karuwar jiragen kasa, bude sabbin hanyoyi, da yawan kayayyaki suka nuna.Jirgin kasan jigilar kayayyaki na kasar Sin da kasashen Turai, wanda aka fara kaddamar da shi a shekarar 2011 a birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar Sin, yana ci gaba da tafiya akai-akai fiye da kowane lokaci a bana, inda ya tabbatar da yin ciniki da safarar kayayyakin rigakafin cututtuka daga bangarorin biyu.A karshen watan Yuli, sabis na jirgin kasan dakon kaya na kasar Sin da kasashen Turai ya kai tan 39,000 na kayayyaki don rigakafin cututtuka, tare da ba da goyon baya mai karfi ga kokarin yaki da COVID-19 na kasa da kasa, kamar yadda bayanai daga kamfanin jirgin kasa na kasar Sin State Railway Group Co. Ltd. suka nuna.Adadin jiragen kasan dakon kaya na kasar Sin da kasashen Turai ya kai matsayin da ya kai 1,247 a watan Agusta, wanda ya karu da kashi 62 cikin 100 a shekara, yana jigilar kayayyaki TEU 113,000, wanda ya karu da kashi 66 cikin dari.Jiragen ƙasa masu fita suna ɗaukar kayayyaki kamar kayan yau da kullun, kayan aiki, kayan aikin likita da ababen hawa yayin da jiragen da ke shigowa ke jigilar madara, giya da sassan mota a tsakanin sauran kayayyaki.

Jiragen jigilar kayayyaki na kasar Sin da kasashen Turai suna yin hadin gwiwa a yayin barkewar cutar

 

 

TOP